Shugaba Buhari ya dade bai dawo ba kusan kwanaki 100. An ce cutar kansa ke damun shugaban. Bayan ‘yan sanda sun tarwatsa ‘yan zanga-zanga, yanzu sun dawo, A kokarinsu na tursasawa shugaba Buhari dawowa ko ma yin murabus, masu zanga-zangar Abuja sun dumfari fadar shugaban kasa, tun bayan da suka sha barkonon tsohuwa daga wurin ‘yan sanda a jiya. Sun sake haduwa ne a dandalin Unity Fountain, wuri da ya zama cibiya ta tirjiya ga gwamnati tun lokacin PDP, musamman lokacin kokarin nemo ‘yan matan Chibok a shekarar 2014. Masu zanga zangar, na dauke ne da takardu da suke kira da ko shugaban ya dawo ko yayi murabus, kamar dai yadda a shekarun baya suka yi wa shugaba Yar’aduwa marigayi. Masu yunkurin tursasa shugaba Buhari murabus sun dunfari adar shugaban kasa Babu dai tabbacin ko hukumomin tsaro zasu barsu su isa fadar ta shugabn kasa, ko kuma zasu nuna musu karfin tuwo, Juglax.com zata bi muku sawu. A yanzu kam shugaba Buhari ya kai wata ukku baya gida Najeriya, kuma duk shekarar nan bayyi wani aiki ba saboda rashin lafiya.