Jamián yan sanda a jihar Sokoto sun hana mabiya akidar Kwankwasiyya kaddamar da wani taro da suka shirya ba tare da dalili mai karfi ba. Da farko dai mabiya Kwankwasiyya sun shirya gabatar da taro a ranar Laraba, 9 ga watan Agusta a kofar Rini bayan sun nemi yardan yan sanda day an sandan farin kaya, sai dai kuma sun samu cikas daga jamián yan sanda a daidai lokacin da zasu fara gudanar da taron. Shugaban Kwankwasiyya na Jihar Sokoto Honarabul Malami Muhammad Galadanci Bajare ne ya sanar da haka a zantawarsa da manema labarai. Dan Majalisa dake wakiltan Mazabar Sokoto ta Arewa Ta (1) a majalisar dokokin Jihar ya bayyana cewa siyasa ce kawai kashin bayan hana masu gudanar da taro. ‘Yan sanda sun hana ‘yan Kwankwasiyya gudanar da taro a Sakkwato A cewar sa wannan shine karo na biyu da ‘yan sanda ke hana masu gudanar da taro. A taron mabiyan na Kwankwasiyya sun tsara rarraba kayan wasannin qwallon kafa ga club- club domin bunkasa sha’anin wasanni tare da karfafa masu guiwa.. Da aka tuntubi kakakin yan sanda na jihar, Ibrahim Muhammad ya bayyana cewa an hana taron ne saboda korafi da jamaár unguwar suka kawo kan abunda ka iya zuwa ya dawo Ya ce babu wani dalili na daban baya ga bukatar da jama’a suka gabatar.