An damke wani Sojan karya a Jihar Niger – Wannan ya faru ne a farkon wancan makon – A Ranar Farfesa Osinbajo ya ziyarci Garin Rundunar Sojin Najeriya ta damke wani Sojan karya kwanakin baya. Wannan abu ya faru ne a lokacin da Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya zo Jihar Neja tare da Ministan ayyuka Babatunde Fashola. An kama wani Sojin karya a Neja An kama wannan Kanal din karyar ne a hanyar Jebba zuwa Mokwa inda yake kokarin zuwa Jihar Kebbi daga Garin Legas a mota. Wani Jami’in MOPOL ne dai ya damke wannan Soja na karya cikin khakin Soja yana karbar kudi daga hannun Jama’a. KU ANAN KUMA : Hanyar zuwa Garin Saraki ta lalace Yemi Osinbajo da Babatunde Fashola a Jihar Neja Idan ba a manta ba dai a farkon makon jiyan Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara Garin bayan wata gada ta karye. Wannan gadar ce ta hada Yankin Kudancin kasar da Arewa. Jiya kun ji cewa an damke masu satar Jama’a su na garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa kaduna kwanan nan. Dama a Watan jiya Sufeta Janar na Rundunar ‘Yan Sanda ya karo ‘Yan Sanda 600 domin takawa masu satar Jama’ar burki domin sa kafar wando tsakanin sa da masu laifi.