Anyi wakar ne domin a sanya tsanar yan Arewa a zukatan yan Najeriya. Gwamnatin tarayya tayi gaggawan daukan mataki -wadanda suka dauki nauyin wakar ba komai ba ne su face yan ta’adda Fitar da wakar sukar kabilan Ibo da ke yawo a arewacin Najeriya “abun kunya ne kuma abun takaice” ,inji Alhaji Balarabe Musa, Tsohon gwamnan jihar Kaduna. Musa ya gaya wa yan jarida Juglax.com cewa wakar bata da nasaba da dabi’un yan Arewa. Ya misalta wadanda suka dauki nauyin wakan a matsayin “Yan ta’adda”, wanda burin su shine janyo tashin hankali da rashin zaman lafiya a Najeriya. Wakar sukar kabilan Ibo, abun kunya ne kuma abun takaici – inji Balarabe Musa Tsohon gwamnan yakara da cewa “anyi wakar ne domin a sanya tsanar yan Arewa a zukatan yan Najeriya. Ya yayi kira da gwamnatin tarayya da su gaggauta daukan mataki saboda barazanar da wakar ke yi ma zaman lafiyar kasan. “Wakar ba abun kunya bane kadai hadda takaici wanda zai iya tada zaune tsaye.” “Gwamnati ta yi saurin daukar matakin hukunta duk wanda ke da hannu wajen daukar nauyin wakar, saboda su ba komai bane face masu yada ta’adanci a cikin kasa.” Ya kara kira da gwamnati da suyi amfani da dukiyar kasa wajen yin adalci, samar da zaman lafiya, kuciyar hankali da karuwan arziki.