Vincent Enyeama ya yi watsi da rokon da ake masa na komawa Super Eagles. An ce ya ki Magana da shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki. Enyeama ya samu sabani da tsohon coach na Eagles Sunday Oliseh wanda hakan ya tursasa yi murabus An rahoto cewa mai kama kwallon Najeriya Vincent Enyeama ya yi biris da rook da ake masa na komawa Super Eagles naa Najeriya saboda gasar kwallon cin kofin duniya da Najeriya zatayi tare da zakaran Afrika Kamaru. Tunda zabin Super Eagles na farko Carl Ikeme na kwace ba lafiya, ada dama yan Najeriya sun shiga damuwar wanda zai tsaya matsayinsa lokacin wasar. Coach na Super Eagles Gernot Rohr ya kuma bayyana cewa zai yi iya bakin kokarin sa don ganin Vincent Enyeama ya dawo kungiyar. Vincent Enyeama Amma rahoton da ke zuwa ma Juglax.com ya bayyana cewa tsohon kyaftin din Enyimba ya yi burus da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kamar yadda ya ki amsa kiran wayar da yayi masa. A cewar rahoto, shugaban kwamitin wasanni na majalisar dattawa Obinna Ogba ya yi bayanin yadda Enyeama ya yi burus das hi da kuma shugaban majalisar dattawa a kokarinsu na rokon shi don ya dawo Super Eagles.