Jam’iyyar APC za tayi taro a jihar Kogi. Kwamishinan yan sadar jihar yayi alkawarin samar da tsaro. Hukumar yansanda gargadi manyan yan siyasa Danagane da taron siyasan jihar Kogi na jam’iyyar APC dake tafe a ranar 11 ga watan Agusta 2017 a Lokoja, Kwamishinan yansadar jihar ya gargadi yan siyasa da su goje daukan masu tada zaune tsaye lokacin taron. Kwamshinan yansandar jihar,Wilson Inalegwu ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labaru. A wani jawabi da mai Magana da yawun yansandar jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar a ranar Talata, yace “Inalegwu ya tabbatar wa jama’a cewa za a yi taron cikin kwanciyan hankali kuma hukuma zata hukunta duk wanda ta kama yana shirin tada zaune tsaye. Taron siyasan Kogi: Yansanda sun garagadi yan barandan siyasa da kada su halarci wajen Jawabin da ya fitar ya kunshi “rundunar yansandar jihar Kogi ta na sanar da Kogi cewa, za a datser wasu hanyoyi a garin Lokoja musamman wajen shataletalen Paparanda zuwa Post Office. “Kuma, duka motocin dake zuwa daga Natako zuwa cikin gari za su iya bin hanyar Naval Headquaters zuwa Post office Junction ko ta hanyar shataletaeln NTA. “Kwamishinan yansandan yayi kira da mutanen jihar da su kiyaye dokoki, kuma ya tabbatar musu da cewa hukumar zata yi iya bakin kokarin ta wajen tabbatar da tsaro da kare dukiyoyi da rayukan al’umma.