Ibrahim Al Amin ya zargi jam’iyyar APC da rashin cika alkawaran da ta daukar ma yan Najeriya Ya ce zai bar jam’iyyar ne saboda mutanen sa. Ya yi ikirarin cewa arewa bata amfana daga shugabancin Buhari ba Ibrahim Al Amin wanda ya kasance jigon jam’iyyar APC a Kano ya sauya sheka zuwa PDP kan rashin cika alkawarin jam’iyyar. Jaridar Cable ta rahoto cewa tsohon shugaban na jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) yace ya bar APC ne saboda jam’iyyar na aikata abunda ta zargi sauran jam’iyyu da aikatawa. Yace: “Koda dai banyi danasanin goyon baya da zabar Buhari ba, bazan ci gaba da kasancewa a jam’iyyar ba saboda basa gudanar da kasar yadda ya kamata. Ina matukar girmama Buhari amma ba shi ke tafiyar da wannan gwamnati ba,” ya fada wa manema labarai a ranar Laraba, “Shugaba Buhari ya rasa iko na gwamnatinsa tun da ya kwanta rashin lafiya. Wasu mutane sunyi amfani da wannan damar wajen tafiyar da gwamnatin. “APC tayi matukar bani kunya saboda ta saba alkawaran da ta dauka ma yan Najeriya. Abunda muka zargi sauran jam’iyyun siyasa da aikatawa, sai gashi APC na aikata su. Talauci na a ko ina sannan APC batayi komai don ceto al’umma daga cikin ta ba. “Na shiga harkar siyasa don na bauta wa mutane na sannan kuma ban jin sukuni kan yadda jam’iyya mai ci ke tafiyar da al’amuran yan Najeriya.” Ya nuna rashin jin dadi kan yadda arewa bata amfana daga shugabancin Buhari ba duk da goyon bayan da suka bashi.