A ranar larabar da ta gabata ne likitocin kasar Birtaniya suka bayyana cewa har yanzu sun rasa gano ainihin abinda ke damun shugaban kasa Muhammudu Buhari Jaridar Juglax.com ta fahimci cewa bayan tsawon watanni na bincike da gwaje-gwaje da kuma kulawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake samu a kasar Birtaniya a wajen likitoci har yanzu ba su iya gano ainihin rashin lafiyar shugaban kasar ba. Daga wata majiya mai karfi ta fadar shugaban kasa, ta bayyana cewa, duk da binciken da gwaje-gwaje na kwararrun likitoci na ciki da wajen kasar Birtaniya har yanzu ba bu wanda ya iya bayyana abin da shugaban yake ciki sai dai kawai ya rasa sha’awar abincinsa ta dauke gaba daya. Rashin bayyanawa ‘yan Najeriya ainihin yanayin kiwon lafiya na shugaban kasa ya shawo kan lamari a cikin kasar ta yadda mutane da dama ke zargin cewa jam’iyyar APC tana aikata laifi irin na abin da ya faru a jam’iyyar PDP lokacin da marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua mulkin kasar nan. Rashin Lafiyar Buhari: Likitoci sun rasa gano abinda ke damun shi “Wadanda ke zargin shugabancin kasancewar tattalin gaskiyar ainihin halin da shugaban kasa yake ciki sun rasa batun da za su fada saboda kawai sai dai su bayyana iya kacin abinda su ka sani. “Kamar yadda a yau, babu wanda ya san irin wannan cuta da ya ke fama da ita. Har ma likitocinsa a Birtaniya ba su san abin da yake ba daidai ba a tattare da shi . Yawancin gwaje-gwajen an yi amma babu wata nasara” Wannan shine dalilin da ya sa likitoci su ka yanke shawara su sanya shi a cikin doguwar kulawa don cigaba da bincikar sa ko za su iya gano matsalar da yake fama da ita.” “Ga wadanda ke kusanci da Shugaba Buhari sun sani cewa ba zai iya zama na tsawon lokaci ba tare da cin abinci ba don ba shi da hakuri tsawaita zama da yunwa, kuma day a ci abinci zai amayar da shi, wannan shine dalilin da ya sanya ba karfi a jikin sa har yanzu. “Daga bayanan da muke samu a wajen likitocin, kowane bangare na shugaban yana aiki daidai. Iyakar matsalar ita ce rashin iya cin abinci saboda yana ci zai amayar. Wannan shine dalilin da ya sa wasu mutane suke zargin cewa an sanyawa shugaban guba ne ko kuma shafi ne irin na ruhanai. Adam Koda yake shugaba Muhammadu Buhari ya kasance mai kwazon aiki a kujerar mulki a shekarar farko tun daga ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015 har zuwa 2016, ya fuskanci wasu kalubale, musamman jinkirin da ya danganci sanya wakilan majalisarsa da batutuwan warware matsalar kasuwancin da ya samu. Tun a karon farko na tafiya kasar Birtaniya don ziyarar likitoci a kan bincikar lafiyar sa, ya rubuta wasika zuwa ga Majalisar Dattawa da ta jagoranci dora nauyin shugabancin kasar nan akan mataimakin shugaban kasar Yemi Osinbajo. Babban mashawarcin Buhari a kan harkokin al’umma, Femi Adesina, ya bayyana cewa wasikar da shugaba Buhari ya rubuta zuwa majalisar dattawar ta yi daidai da sashe na 145 (1) na kundin tsarin mulkin Najeriya. Adesina ya shawarci ‘yan Najeriya game da rashin lafiyar shugaban kasa da kuma bukatar kada kowa ya tashi hankalinsa akan rashin lafiyar ta shugaban kasa. Kamar yadda aka sani kuma, ya rubutawa shugaban majalisar Dattijai, Bukola Saraki da Shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara,wasika ta bankwana a yayin tafiyar ta shi zuwa kasar Birtaniya a ranar 23 ga Janairun 2017. ‘Yan Nijeriya sun nuna tausayawa kuma sun fahimci cewa shugaban na bukatar kulawa da lafiyarsa kafin ya dawo ya cigaba da daukar nauyin shugabancin kasar nan.