Kungiyar Jama’atu Nasir Islam ta yi da zargin dattawan kirista na kasa – Kungiyar ta ce zargin ajanda na musuluntar da Najeriya ba gaskiya ba ne –

Sakataren kungiyar ya ce kalaman wata hanyar karkatar da hankalin mutane daga kisan kiyashi da aka yiwa al’ummar musulmai a jiyar Taraba ne Kungiyar Jama’atu Nasir Islam (JNI) ta yi watsi da kalaman janar T.Y Danjuma mai ritaya da kuma dan kungiyar dattawan kirista na kasa NCEF cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na kokarin musuluntar da Najeriya.

Idan dai baku manta ba a makon da ta gabata neJuglax.com ta kawo muku rahoto cewa kungiyar dattawan kirista na kasa sun zargi shugabanin addinin musulunci da wata ajanda na musuluntar da kasar Najeriya.

A lokacin da suka mai da martanin kan zargin, kungiyar addini musulunci a karkashin jagorancin sarkin musulmi sun yi Allah wadai da kalaman dattawan, kuma abin mamaki a ce kamar T.Y Danjuma da wasu shugabanin addinin kirista suka fito da irin wannan kalaman.

Mabiyar addinin Islama Babban sakataren JNI, Dr. Aliyu Abubakar-Khalid, wanda ya yi magana da manema labarai a Kaduna a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli ya ce wannan wani hanyar karkatar da hankalin mutane daga kisan kiyashi da aka yiwa al’ummar musulmai a jiyar Taraba.

Sakataren ya ci gaba da cewa irin wannan kalaman bai da ce da dattawan ba. Ya ce, in har akwai wani kirista da aka tilastawa ya yi ridda a kasar zai su fito su yi bayani