Rikicin keta haddi a tsakanin wasu ma’aurata ya sanya sun jefa jaririn su dan watanni tara da haihuwa cikin wuta inda ya soye fuskarsa da mikamikin sa. A ranar talatar da ta gabata ne wani tsohon direba, Igwe Dike mai shekaru 42, ya gurfana a gaban kotun majistire ta Ikeja dake jihar Lagos, da laifin lakadawa matar sa Nkiru Egbo, mai shekaru 35 duka da katako wanda hakan ya raunanata ita da jaririn ta na goye. An kama Dike akan tuhumar laifuka biyu na cin zarafi da raunana jikin dan Adam wanda ya ce shi bai amsa wannan laifuka da ake tuhumar shi da su ba. Jami’in dan sanda Simon Omhowa, mai karar wannan mutum ya bayyanawa kotu cewa wannan abu ya faru ne a ranar 30 ga watan Yuli a gidan na su na zaman aure dake Layin Ferry na unguwar Mil biyu dake jihar ta Legas. Wasu iyaye sun jefa jaririn su dan wata 9 cikin wuta sanadiyar rikicin keta haddi Ya ce wannan laifuka da wannan mutum ya yi sun saba ka’idoji da karya doka karkashin sashe na 170 da 171 na kundin tsarin dokar aikata miyagun laifuka na jihar Lagos ta 2011. Ita ko matar ta shi ta bayyanawa kotu cewa, mijin na ta ya biyo ta ne da adda wanda a yayin arcewa ne ta yar da jaririn su dake goye a bayanta, dan watanni tara a duniya cikin wuta inda ya soye fuskarsa da mikamikin shi na dama. A yayin da shi kuma Dike ya ke bayyanawa kotu na shi rahoton, ya ce, sun yi aure ne tun a shekarar 2006 inda auren na su ya albarkatu da ‘ya’ya uku kuma su na zaune cikin farin ciki tun daga wannan lokaci har zuwa lokacin da ya rasa aikin shi a shekarar 2016. Ya ce, “a ranar da wannan abu ya faru da misalin karfe 12:30 na dare, na dawo na riski mata ta da wani mutum a cikin wata mota a kofar gida na su na saduwa irin ta aure “Ban yi wata-wata ba na dauki sanda, na bude mirfin motar kuma na buga katakon a kan wannan mutumi. “A wannan hali ne matar ta wa ta yi kokarin kwace sandar da ke hannu na inda shi kuma mutumin ya samu dama ya arce” “Mun yi ta kici-kici da ita har dai na ci karfin ta kuma na lakada ma ta duka da wannan sanda, wanda hakan ya sa ta gudu ta je makwancin jaririn na mu ta yakito shi cikin sauri wanda garin gudu ta fadi kuma jaririn ya fada cikin wuta.” Faruwar wannan abu ne matar Dike ta kai kara ofishin ‘yan sanda wanda hakan ya yi sandiyar cafke shi, inda alkali mai shari’a a kotun majistire ya bayar da belin shi akan kudi Naira 100, 000 kuma ya daga shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Agusta.