Uwargidar shugaban ƙasa Aisha Buhari ta samar da wata cibiyar karbar magani da kwantar da marasa lafiya. Aisha Buhari ta gina asibitin ne domin taimaka ma mata masu juna biyu Manufar uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari na samar da kasaitaccen Asibiti a garin Daura, mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu tagomashi yayin da aka kusa kammala aikin ginin asibitin. Idan ba’a manta ba dai, tun a watan Mayu na shekarar 2017 ne uwargidar shugaban kasar, ta sanya bulo na kaddamar da ginin asibitin, wanda aka kirkireshi a cikin babban asibitin Daura, kamar yadda Kaakakin ta, Suleiman Haruna ya bayyana. Juglax.com ta samu rahoto cewa manufar gina asibitin shine domin rage radadin wahalhalun da mata masu juna biyu ke fuskanta musamman wajen haihuwa da kuma yayin rainon yara. Asibitn Bugu da kari Aisha Buhari ta gina asibitin ne mai cin gadaje 50 domin goyon bayan manufar gwamnatin mijinta na ganin ta gina asibitoci a kowanne mazaba dake dukkanin fadin kasar nan.