Rundunar Sojin Najeriya ta mayar da wasu sojoji gida daga filin yaki. An kwashe Sojojin ne da suka dade suna fafatawa da yan Boko Haram. A kokarinta na tabbatar da an sauya ma Sojojin da suka dade a bakin daga suna yaki da mayakan yan ta’adda wurin aiki, rundunar Soji ta mayar da wasu Sojoji barikinsu dake fatakwal. Sojojin da suka fito daga bataliya ta 29 sun koma gida ne biyo bayan wani umarni da babban hafsan Sojin kasa, Laftanar Tukur Yusuf Buratai ya bayar da a sada su da iyalinsu, wanda hakan yayi matukar faranta musu rai. Sojojin na daga cikin wadanda suka rayu bayan kwashe shekaru da dama suna yaki da yan ta’adda, a jawabinsa, kwamandan runduna ta 6, Manjo janar EO Udoh yayi ma Sojojin maraba da dawowa gida, sa’annan ya jinjina musu. Matan Soja Juglax.com ta ruwaito kwamandan ya bukaci da su taya abokanan aikinsu da suke bakin fama da addu’a domin samun nasara akan yan Boko haram, sa’annan ya shawarce su dasu dage wajen bada gudunmuwa a duk lokacin da aka kiraye su.