• Manyar Bangaren Kudancin Kasar nan sun yi taro game da matsayar Najeriya – Mutanen Kudu sun koka game da yadda Makiyaya su ka addabi Jama’a – Mutanen Yankin Arewa ne kurum ba su halarci wannan taron ba Za ku ji labarin cewa mutanen Kudancin Kasar da Arewa maso tsakiya sun yi wani taro inda su ka kira ayi wa Najeriya garambawul domin kowane sashe ya ci gajiyar albarkun kasar da kyau. Mutanen Kudu sun yi taro game da matsayar Najeriya Cif Edwin Clark da Cif Ayo Adebanjo da Janar Nwachukwu Ike da Janar Jemibewon David su ka wakilici Yankin su inda su ka nuna rashin goyon bayan a raba kasar. Manyan kasar sun ce bukatar su ayi wa Najeriya garambawul. KU KARANTA: Gobara ta hallaka Jama’a a Kalaba An koka game da Makiyaya Fulani Wadanda su ka halarci taron sun koka game da yadda Fulani Makiyaya su ka addabi Jama’a. Mutanen su kace babu bambanci sosai tsakanin ‘Yan ta’addan Boko Haram da Makiyayan na Fulani. Wannan makon kun ji cewa Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya nemi a sauya tsarin Najeriya domin Jihohin Kasar 36 su kara karfi fiye da yadda ake yanzu. Atiku yayi wannan jawabi ne a wani taro da aka yi game da batun raba kasar a Abuja.