Labarin da muke samu yanzu da dumi-dumin sa yana nuni da cewa ana zaman jiran tsammanin isowar jiragen ruwa 27 makare da man fetur da kayayyakin abinci a tashar jiragen ruwan Najeriya dake a jihar Lagos. Hukumar gwamnatin tarayya dake kula da tashoshin ruwan kasar karkashin jagorancin Hadiza Bala watau Nigerian Ports Authority (NPA) a turance ce ta bayyana wa manema labarai hakan yau litinin. Juglax.com ta samu labarin cewa hukumar dai ta bayyana kayan abincin da za su iso da suka hada da alkama, kifi, masara, takin zamani da kuma albarkatun man fetur da suka hada fetur din kan sa da bakin mai da man gas da man jirgi da dai sauran su. Haka ma dai hukumar ta kara da cewa dama dai tuni wasu jiragen da suka kai 9 sun iso gabar ruwan Najeriyar inda suke jira a sauke kayan da suke dauke da su na masarufi.