Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa yayi gargadi da yan Najeriya su guji yadda kalmomin battanci ga junan su. Atiku Abubakar yayi tir da wakan tsanan al’ummar ibo da ke yawo a gari. Atiku Abubakar yayi kira ga hukuma da su zakulo wandanda sukayi wakar kuma a hukunta su Tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria kuma jigo a jam’iyyar APC yayi kira ga yan Nigeria dasu guji aikata duk wani abu daka iya saka Nigeria cikin rikicin kabilanci kamar yadda ta taba faruwa kasar Rwanda. Atiku ya gargadi yan Nigeria dasu guji fadawa irin rikicin daya faru kasar Rwanda Yayi gargadin ne jiya a wani jawabi daya raba ga yan jarida. A cikin jawabin nasa, ya bayyana rashin jin dadinsa a kan wata wakar hausa ta cin mutunci ga kabilar igbo dake yawo a gari. Yayi tir da wakar kuma yayi kira ga duk yan kasa na gari da suyi watsi da duk lamarin da zai iya kawo rabuwar kawuna. Wazirin na Adamawa ya kara yin kira ga jami’an tsaro dasu zakulo tare da hukunta wadanda suka wallafa wakar wacce ke nuna tsana ga kabilar ta Igbo. Atikun yace, rikin kisan kare dangi daya faru a kasar Rwanda ya fara ruruwa ne daga wata waka mai taken “Nanga abahutu” (na tsani kabilar Hutu) wacce wani shahararren mawaki dan kabilar tutsi mai suna Simon Bikindi ya wallafa. A karshe yayi addu’ar Allah ya kiyaye Nigeria daga fadawa kwatankwacin rikici irin wanda ya afku a Kasar ta Rwanda.