An kara hurowa Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo wuta da ware Musulmai a wani sabon kwamiti. Kwamitin zai duba irin badalar da Sojoji ke tafkawa fama da Boko Haram. A cikin kwamitin da aka nada babu wani Musulmi ko Dan Yankin Borno. Juglax.com Hausa na da labari cewa an kara hurowa Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo wuta game da dai nade-naden sa ba. Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta nada wani kwamitin mutane 7 da zai duba irin badalar da Sojoji ke tafkawa wajen Yakin Boko Haram a Najeriya. Duk cikin wannan kwamitin babu wani Musulmi ko wani Dan Yankin Borno ko guda. ‘Yan Arewa sun hurowa Osinbajo wuta Alkali Biobele Georgewill ne Shugaba wannan kwamiti. Saura sun hada da Wale Fapohunda, Ifeoma Nwakama, Janar Patrick Akem dsr. Kaf dai a wannan Kwamiti babu wani dan Area maso gabas na Borno, Adamawa ko Yobe sai dai wani Dan Jihar Gombe. Saura irin su Jibrin Ibrahim dai Kirista ne kuma Dan asalin Kano yayin da Hauwa Ibrahim kuma ita ma ta bar Musuluncin don haka ne wasu mutanen Yankin da abin ya shafa su ka ce Musulmai abin ya fi shafa don haka ya kamata su yi ruwa da tsaki