Khalifa Isyaka Rabiu (Khadimul Kur’an), babban dan kasuwa kuma mahaifi ga Abdulsamad mai kamfanin BUA ya yi yinkurin samar da sabuwar jami’a a jihar Kano mai suna AT-TANZEEL UNIVERSITY. Khalifa Isyaka Rabiu, Shahararren dan kasuwar nan kuma mahaifi ga Abdulsamad mamallakin kamfanin nan mai suna BUA, ya bayyana kudirin sa na samar da sabuwar makarantar jami’a mai suna AT-TANZEEL UNIVERSITY a jihar Kano. Zaá samar da makarantar ne domin ta mayar da hankali gurin horar da dalibai mahaddatan littafi mai tsarki wato Al-Qur’ani mai girma. Tuni dai anyi nisa wajen kaddamar da wannan makaranta, kamar yadda nan dad an wani lokaci kadan zaá gudanar da bikin bude makarantar tare da fara karantar da dalibai a cikinta. Kano: Sheik Isiyaka Rabi’u zai samar da jami’ar mahaddata Qur’ani. Wannan alámari yayi ma jamaár musulmi dadi, inda suka nuna godiyarsu da kuma fatan Allah ya kara kawo wadanda zasuyi koyi da wannan bawa.