Kungiyar Buhari Media Support Group, ta sanar da tarin aiyukan raya kasa da inganta rayuwar al’umma da za’a aiwatar da tarin kudin da aka kwato a hannun tsohuwar ministan man fetur a gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Diezani Alison Madueke. Kamar yadda kuka sani an zargi Diezani Alison da satar wasu makudan kudade a lokacin da take a matsayin ministar ta man fetur. A cewar kamfanin dillanci labarai ta Najeriya (NAN) Shugaban kungiyar Austin Braimoh da Sakataren sa Cassidy Madueke, sun sanar cewa za’a iya gina manyan filayen sauka da tashin jiragen sama irin wadanda duniya ke tinkaho da su, dai-dai har guda shida. Sun kuma kara da cewa a cikin kudaden za’a iya kaddamar da gagarumin shiri na ingata harkar mona a cikin kasar, wanda zai samar da tarin ayyukan yi ga matasa. Har ila yau, sun kara da nunin cewa daga cikin naira bilyaN 42.7 da kuma Dala milyan 487.5 na zunzurutun kudaden da EFCC ta gano a hannun ta, za a iya karasa aikin titin jirgin kasa daga Lagas zuwa Kano da kuma Lagas zuwa Calabar. A baya Juglax.com labarto muku cewa kotu ta kwace wadannan kadarori, amma na wucin gadi ne, yanzu dai kwacewar ta din-din-din ce. Wannan na biyo bayan irin wannan mataki da gwamnatoci ke dauka a sauran kasashen duniya kan kadarorin ita Diezanin da ma wadansu yaranta. A karar da hukumar EFCC dai ta shigar, ta fitar da bayanin cewa kudi hannu a buhu-buhu Diezani ta biya ta sayi dogon benen a shekarar 2013, dai-dai lokacin da shugaba Jonathan ke ta fada da Sarkin Kano Sunusi Lamido lokacin yana gwamnan CBN, kan fadinsa cewa Diezani barauniya ce. Wanda hakan ya janyo masa rasa kujerarsa.