Ibrahim Magu Shugaban EFCC yace babu gudu babu ja da baya a yaki da rashawa. Shugaban hukumar yaki da almundahana da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Malam Ibrahim Magu ya bayyana cewa duk yawan kudaden da hukumar ta kwato daga hannun tsohuwar ministan mai, Diezani Allison Madueke somin tabi ne kawai. Magu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 10 ga watan Yuli a lokacin dayake tattaunawa da gidan talabijin na TVC, inda ya bayyana cewa sun kwato akalla naira biliyan 47.2 da kuma gidajen da darajarsu ta kai $487.5 daga wajen Diezani. Magu yace bayyana ma majiyar Juglax.com cewar a yanzu haka suna yin wani aikin gwiwa tare da hukumomin yaki da rashawa a kasashen duniya domin hako kudaden da ta sace ta kai su kasashen waje. Ibrahim Magu “Muna aikin kwato dukkanin kudaden data sace, tare da kama sauran mutanen da tayi aiki dasu.” Inji Magu. Sa’annan ya ce babban kalubalen dayake fuskanta shine yadda ake ci masa dudduniya a aikinsa. Diezani Daga karshe shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu yace babu lokacin dayafi dacewa a yaki cin hanci da rashawa a Najeriya kamar yanzu, don haka yake bukatar goyon bayan yan Najeriya.