Idan bamu sa dokan yin finafinai da wakoki a cikin gida ba matasan mu za su rasa aikin yi Dokan zai daga darajar harkan wasanni a Najeriya – Lai Mohammed yana alfahari da kamfanin COSSON Gwmanatin tarrayya na yunkurin canza dokan watsa shirye-shirye dan hana yin finafinai da wakokin gida a kasashen waje. Minitsan labarai da Al’ada Lai Mohammed ya tabbatar da hakan a ranar Asabar lokacin da ya kai ziyara ofishin “copyright society of Nigeria”. Ministan ya koka akan yin finafinai da wakokin cikin gida domin yan kasa a kasan waje. Gwamnatin Najeriya zata hana yin finafinai, da wake-waken gida a kasan waje Yace al’amarin yaja ci baya wajen rashin karfafa samun gwanaye a wasanni, da kuma rashin cigaban masan’antar da rashin tallafa wa tattalin arziki kasa ga baki daya.“ Wannnan gwamnatin ta yake hukunci cewa duk finafinai da wakokin gida dole ayi su a cikin kasan nan. Dan karuwar kasan. Bai dace muci gaba da yin finafinan gida a kasan Afrika ta Kudu ko wani kasa ba, sannan a sayad da shi a Najeriya. ” Kungiyan watsa finafina da tallace-tallace sun bayyana al’amarin karara. Yace abun dake faruwa a kasannan a yau shine ana fitar da yan wasa kasan waje dan yin finafinai da rikodi wakoki . Idan suka je waje, suna siyan duk wani abun da suke amfani da shi wanda ke karfafa tattalin arzikin kasashen. sai kuma su dawo nan gida su sayar da shi. Yace: “Idan bamu sa dokan yin finafiai da wakoki a cikin gida ba, matasan mu za su rasa aikin yi Yan Najeriya ke kallo ,sauraro da siyan finafinan da wakokin da suke yi saboda haka dole ne kasan ta karu da su. Zan hadu duk wani mai ruwa da tsaki wajen ganin an samu nasarar canza dokan cikin gaggawa.” Dan karfaffa harkan finafinai da wakokin gida, minitsa yace hukuman daukaka hanun jari za su hada hannu dan ganin cigagban masana’antu. Ministan yace daga yanzu akwai sharuddan shigowa da kayan fina-finai da wake-wake. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasan ta dau alwashin ganin yiwuwar masana’aantar da kuma ganin ya anfanarda alumma. Lai Mohammed yace masana’antar wasanni yana daya daga cikin hanyoyin karfafa tattalin arzikin kasa saboda haka gwamnati zata bada nata gudunmawan wajen ganin an samu cigaba a fannin. Ministan ya yabi COSON da ma’aikatan ta wajen samun nasara tunda aka kaddamar dasu shekara bakwai da ya gabata. “Ina matukar farin ciki da alfahari da COSON, saboda gwanintar su da iya aiki me kyau wanda babu shakka zasu iya karawa da kamfanonin kasashen waje.” Kamfanin tayi aiki mai kyau wajen kare hakkin kamfononin finafinai tun lokacin da aka kaddamar da su a shekara 2010. Lai mohammed ya ziyar ci headkwatan COSSON dan duba kayan aikin su. Shugaban COSON Tony Okoriji. Yace kungiyansu Kaman lema ce mai kare hakkin mutuncin yan harkan wasanni. A cikin wa yanda suka ziyar ce wajen tare da ministan har da darektan NTA Yakubu Mohammed, da shugaban FRCN Mansur Liman.