A cikin dalilin nadin Ibrahim Magu ga Chairman EFCC,  Gwamnatin Buhari za ta kai Sanatoci Kotun koli – Sanatocin kasar sun tubure cewa dole Magu ya bar Ofis tun da ba a tabbatar da shi ba – Fadar Shugaban kasa dai tace babu abin da zai sa a cire Ibrahim Magu daga EFCC Ku na sane cewa ‘Yan Majalisa sun tubure cewa dole sai Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu ya bar Ofis tun da ba a tabbatar da shi ba wanda yanzu wannan maganar za ta kai ga Kotun kolin kasar. Hoton Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu a Ofis Ana ganin cewa Gwamnati za tayi nasara idan aka shiga Kotu. ‘Yan Majalisar Kasar har bore sun yi a kan cigaba da zaman Magu a Ofis. Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Osinbajo ya nanata cewa Majalisa ba ta da hurumin cewa Ibrahim Magu ya bar Ofis. KU KARANCI KUMA: Tsohuwar Ministar mai ta shirya zuwa kurkuku Gwamnatin Tarayya na tare da Magu Kan dai manyan Lauyoyin Kasar ya rabu inda wasu ke ganin Gwamnatin Tarayya ba tayi laifi ba yayin da wasu ke ganin an yi babban sabo wanda hakan na iya jawo a ma tsige Shugaban kasar gaba daya. Ku na sane cewa tun bayan tafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari har yau ba a ga hoton sa ba illa dai wani sakon da ya aiko lokacin bikin karamar Sallah ga Musulman kasar.