Jaridar Juglax.com ta Ruwaito yadda fadar shugaban kasa ta ki dora mace mukami. Majalisar Dattijai ta tantance Hajiya Dr. Asma’u Sani Maikudi. Hukumar zabe na shirin tunkarar jam’iyyu kan yadda zasu yi zaben cikin gida. A cewar jaridar Juglax.com, fadar shugaban kasa ne ke jinkirin mika wa Dr Asma’u Sani Maikudi takardar shaidan fara aiki bayan majalisan dattawa sun tantance ta tun makonni uku da suka wuce. Dr Maikudi dai yar asalin jihar Katsina ne kuma shugaba Buhari ne ya zabe ta tare da wasu mutane guda 26 domin cike gurabe 27 a sauran jihohin Najeriya. Fadar shugaban kasa ta dakile damar mace tilo a hukumar zabe ta INEC Duka mutanen da shugaba Buhari ya zaba tuni sun samu tantancewar hukumar binciken sirri na DSS da kuma kotun da’an ma’aikata kafin majalisan dattawa tayi na’am dasu a 20 ga watan Yuli. A cewar jaridar Juglax.com, sauran mutanen da majilisan dattawa ta tantance duk an basu takardun shaidan fara aiki daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya amma ba’a baiwa Dr Maikudi ba. Wani babban jami’in gwamnati yace fadar shugaban kasa ne ya kamata ta aika da sunayen wadanda majalisan dattawa ta tantance zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya kafin a mika musu takardan shaidan fara aiki, saboda haka matsalar daga fadar shugaban kasa ne. Bisa ga dukkan alamu, akwai wadanda ke da kokwanto akan mika sunan ta daga fadar shugaban kasa, a cewar babban jami’in gwamnatin. Da aka nemi ja ta bakin fadar shugaban kasan, babban mai taimaka wa shugaban kasa a harkokin da suka shafi majalisa, Senata Ita Enang yace ba zai iya tsokaci akan lamarin ba domin bai san komi akan lamarin ba. Ra’ayoyin lauyoyi ya banbanta akan lamarin, wasu suna ganin Dr Maikudi bata da ikon shigar da kara kotu tunda dama ba’a riga an bata aikin ba amma wasu suna ganin akwai tauye haki a ciki kuma tana iya tursasa ofishin sakataren gwamnatin su bata takardan shaidan fara aikin. Wasu kuma suna ganin ana yi mata wala-wala ne kawai domin ita mace ce.