An fara zanga zangar wai lallai Buhari ya dawo ko ya sauka daga mulki a Abuja. Yan-sanda sun ce baza su lamunta ba, sun tarwatsa masu karajin. A baya ma dai shugaba ‘Yar-aduwa ya fuskanci irin wannan lokacin jinyarsa An ji wa mutum daya rauni a ranar Talata a Abuja sanda ’yan-sanda suka jefa barkonon ’yar-tsohuwa cikin ’yan zanga-zangar masu cewa Shugaba Buhari ya dawo gida ko kuma yayi murabus daga karagar mulki. ‘Yan zanga-zangar Buhari ya dawo gida ko ya sauka – Hoto daga Punch Nigeria. Buhari ya bar Najeriya tun watan Mayu 2017 a kan neman lafiya a birnin Landan. Mutumin da aka jiwa ciwo ya an kai shi asibitin da ke cikin sakateriyar kasa da ke kusa filin zanga-zangar. Har yanzu da ba’a san iyakacin tsananin raunin ba. ’Yan zanga-zangar sun yada zango ne a cikin filin shakatawar Mileniyum dake kusa da Unity Fountain, Abuja, sanda ’yan-sandan suka zo tarwatsa su. Amman hakan ya ci tura inda suka tsaya tsayin daka suka ki motsawa har tsawon awa daya bayan zuwan ‘yan sandan.’Yan zanga zangar sun hada daga cikin kungiyoyi daban-daban na mazauna Najeriya, kuma takensu shine ko Buhari ya dawo gida ko kuma ya sauka daga kujerar mulki in ba zai iya ba.