Direbobin taxi a kan jihar Ondo sun kawo tsaikon harkokin yau da kullum a jihar sanadiyar karin kudin tikiti da kungiyar ma’aikatan zirga-zirgar tituna ta janyo Mazauna babban birnin Akure na jihar Ondo sun shiga cikin halin kakanikayi a ranar larabar da ta gabata bayan da direbobin tasi su ka shiga zanga-zanga da yajin aiki sanadiyar karin kudin tikiti da kungiyar ma su sana’ar zirga-zirga, (National Union of Road Transport Workers) ta kara daga Naira 200 zuwa 350. Tun daga karfe 8:00 na safiyar ranar larabar da ta gabata, direbobin tasi su ka hada gangami na zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin yadda ake tafi da shugabancin kungiyar NURTW a jihar wanda su ka ce a na almundahana daga karbar shugabancin da bai wuce sati uku. Da yawa daga cikin direbobin sun yi ta tsayar da ‘yan uwan su direbobin tasi da su ka dauko fasinjoji a kan lallai sai sun sauke su domin su ma su shigo a yi zanga-zangar da su. Direbobin tasi sun shiga zanga-zangar karin kudin tikiti Wannan abu ya haifar da tsaiko matuka a jihar sanadiyar kashe hanyoyi da direbobin tasin suka gudanar a manyan tituna. Direbobin tasin su na kira akan a rage wannan kudin tikiti kuma sun ce ba su son sake karbar wani tikitin kananan hukuomin jihar. Kuma su na kira da kungiyar ta su tda ta yi karin kudin hayra tasi daga naira 50 zuwa 100 don su samu hanyar da maye gurbin kudin tikitin da kungiyar ta kara. Wani direban na tasi, Femi Adebayo, ya na tuhumar shugabannin kungiyar da cin hanci kuma ya ce wanda su ke sayan tasi don a yi mu su haya sun gaji da wannan ka’idoji na kungiyar. Da yawa daga cikin fasinjoji sun koka da wannan karin kudin tikiti inda su ka bayyana cewa wannan zai janyo wahalhalu wajen kari na kudin hayar tasi.