Olusegun Obasanjo tsohon shugaban kasa, yace mahaifinsa ne ya rinjayi raáyinsa don ya yi karatu, Obasanjo ya bayyana cewa saura kiris wani sabani day a samu da wani malamin sa ya kawo karshen karatunsa Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda girmamawa da yake wa mahaifinsa ya sa shi marin malaminsa a ranar sa na farko a makaranta. Da yake Magana a ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta a wani taro a jihar Lagas, tsohon shugaban kasar ya ce ya mari malamin sa a lokacin day a tambaye sa sunan mahaifinsa wanda a ganinsa cin mutunci ne, jaridar Juglax.com ta ruwaito. Da yake bada labarin yadda alámarin ya afku, Obasanjo yace: “Na kasance ina bin mahaifina gona amma wata rana, sai ya tambaye ni abunda nake burin yin sai na fada masa zan so na zama makanikin. Amma sai ya kawo shawarar karatu sai aka sani a ciki. “Munje Abeokuta tare sannan muka kai ziyara makarun biyar amma duk suka ki karba na saboda sun rigada sunyi nisa a karatu. Dalilin da ya sa na mari malamina a makaranta – Obasanjo “Daga baya sai aka kaini wani makaranta da basu yi nisa ba. Amma, a ranar farko a makarantar, sai suka tambaye ni sunana na fada masu amma a lokacin da suka tambayi sunan mahaifina, sai na ji abun banbara kwai. “A yanda aka taso dani a kauye, idan mutun ya ambaci sunan mahaifinsa toh hakan kamar cin mutunci ne don haka day a tambaye ni sunan mahaifina sai na ga abun a matsayin cin mutunci. Don haka, sai na mare shi sannan kuma aka hukunta ni a kan haka.” A cewar tsohon shugaban kasar, wannan sabani da ya shiga tsakaninsa da malamin ya kusa kawo karshen karatunsa amma sai Allah ya shiga lamarin.