Liverpool ta yi watsi da tayin fam miliyan 90 da Barcelona ta yi don neman sayen madugun ‘yawan wasan kwallon kafa na Brazil Philippe Countinho.

Tayi na biyun da Barca ta yi wa dan wasan mai shekara 25, wanda aka ki amincewa da shi nan take, na kunshe da biyan fam miliyan 76.8 da farko sannan a kara fam miliyan 13.5 daga baya. Liverpool ta nananta cewar Coutinho – wanda ya koma wurinta daga Inter Milan kan kudi fam miliyan 8.5 a shekarar 2013, ba na sayar wa ba ne. Barcelona ta sayar da dan wasan gaba na Brazil, Neymar, ga Paris St-Germain kan kudi fam miliyan 200, ciniki mai cike da tarihi da ba a taba yin irinsa ba a makon jiya. Philippe Coutinho, wanda ya ci kwallo 14 a kakar da ta wuce kuma ya yi jinyar idon sawu na mako shida, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara biyar a watan Janairu.