Buratai ya karrama jaruman Sojojin Najeriya a jihar Borno. Sojojin sun cancanci yabo ne bayan wani artabu da suka yi da yan Boko Haram Babban hafsan sojin kasa, laftanar janar Tukur Yusuf Buratai ya karrama wasu jajirtattun Sojojin Najeriya manya da kanana a ranar Talata 8 ga watan Agusta da lambobin yabo sanadiyyar jarumata da suke nunawa a fagen yaki. Wata sanar data samu sa hannun mataimakin jami’in hulda da jama’a na runduna ta 8 dake Maiduguri, laftanar kanal Kingsley Samuel ta bayyana cewar an karrama hafsan soji guda 2 da kananan sojoji su 61 bayan wani artabu da sukayi da yan ta’addan Boko haram har sau biyu a watan Yuli. Su dai wadannan Sojoji da suka samu lambar yabo sun samu kansu ne cikin tarkon yan Boko Haram yayin wata kwantar bauna da suka yi musu, amma duk da haka sai da suka fice daga wannan tarko, kuma suka bude ma yan ta’addan wuta, suka hallaka su, har ma suka kwashi ganiman makamai. Buratai Yayin da yake karrama sojojin, Buratai ya yaba da jarumtar Sojojin, inda ya bayyana aikin soji tamkar bauta ce ga kasa, sa’annan ya taya rundunar Sojin murnan nasarorin da suka samu, kuma ya bukaci da kada su yi kasa a gwiwa a kokarin da suke yi. Buratai Juglax.com ta ruwaito Buratai ya kai ziyarar aiki a bataliya ta 202 dake Awulari, kan hanyar Bama inda ya lura da yadda Sojoji ke amfani da makamai, sa’annan ya zarce Madatsar ruwa dake Alau kan hanyar Konduga don gane ma idanunsa yadda Sojoji ke gudanar da sintiri a ruwa.