Bola Ahmed Tinubu Jigon APC, ya fadi cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na samun lafiya sosai – Tinubu ya ce kwanan nan a zuba ido da dawowar Buhari gida – Ya kuma yi magana a kan zargin rikicin mulki tsakanin mukaddashin shugaban kasa da majalisar dattawa Tsohon gwamnan jihar Lagas kuma babban jigon jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya ce shugaban kasa Buhari na samun sauki cikin sauri kuma zai dawo gida nan ba da jimawa ba. NAIJ.com ta tattaro cewa Tinubu, ya yi wannan jawabi ne a lokacin wani ziyara na ta’aziya da ya kai ma gwamna, Abdullahi Ganduje, kan rasuwar Maitama Sule. A cewar wata rahoto daga jaridar Premium Times, Tinubu ya ce: “Koda dai ni ba kakakin shugaban kasar bane sannan kuma bana daga cikin tawagar fadar shugaban kasa, shugaban kasar na samun sauki sosai sannan kuma idan Allah ya yarda, zai dawo nan ba da jimawa ba.” Buhari zai dawo nan ba da dadewa ba inji Tinubu KU KUMA KARANTA: Shugaba Buhari ya aika sako ga mutanen Jihar Sokoto A kan rikicin mulki dake tsakanin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo da kuma majalisar dattawan Najeriya, Tinubu ya ce: “Na taba kasancewa a gurin sannan kuma abunda ke faruwa ba wani abun tashin hankali bane, yak an faru a damokradiya. Bangaren zartarwa na da rawar da take takawa sannan kuma bangaren dokoki na da nasu rawar ganin, duk suyi aiki don ci gaban kasar.” Rashin shugaba Buhari a kasar na ta haifar da cece-kuce a fadin kasar harma ta kai da daman a neman ya yi murabus.