Yan bindiga sun kashe makiyaya hudu a kudancin kaduna – tayi kira da mabiyanta da kada su dauki doka a hanun su -Yansanda ba su ce komai ba game da abun da ya faru Yan bindiga sun kashe makiyaya yan fulani guda hudu a karamar hukumar Kajuru dake jihar Kaduna. Har ila yau hukumar yan sanda basu ce komai game da abun da auku ba. Sakataren kungiyan makiyayan Najeriya na Miyyeti Allah, Abdullahi Ibrahim ya fada ma manema labarai a ranar Asabar cewa bayan aika-aikan da yan bindigan sukayi sunyi awon gaba da yan fulan guda biyu. Yan bindiga sun kashe makiyaya hudu a kudancin Kaduna Ya kuma kara dacewa yan bindiga wa yanda har ila yau ba a san ko su waye ba sun kara kai hari unguwan Tsohon Dimshi da ke karamar hukuman Chikun na jihar in da suka kara da rusa musu gidaje. A yayin da yake bayyana abun da yafaru cikin fushi da bakin ciki, Sakataren Miyyeti Allah yana kira da mabiyansa da su yi hakuri kada su dauki doka a hanun su , su bar hukuma tayi aikin ta wajen kama wa yanda suka aikata ta’adancin.